Wani gari wanda basa amfani da kudi wajen yin kasuwanci a Nigeria

0

Ko kunsan akwai wani garin a dake cikin Nigeria wanda su har yanzu basa amfani da kudi wajen gabatar da harkokin kasuwancinsu saidai suna bada wani kayan sannan su karbi wani kayan, ina nufin idan kaje kasuwar da kayanka saidai ka samu wani da yake bukatar irin kayan naka ka bashi sai ya baka nasa wato kasuwancin da ake cewa bani gishiri in baka manda kenan?

A cikin wannan rahotan zamu sanar daku sunan garin da kuma jihar a cikin Nigeria.

Kauyen Mai suna Esuk MBA wani dan karamin guri ne da wasu mutane ke zama sannan kuma da kasuwa a gurin wacce take ci sau daya a sati, kauyen yana karkashin karamar hukumar akpabuyo ne dake jihar Cross rivers, wanda su har yanzu suna gabatar da kasuwancinsu ne kamar na zamanin baya wato wanda ba’a amfani da kudi.

Inda suke daukar kayansu sukai kasuwa sai kuma su samu wanda yake son kayan ka bashi idan kayan da yake gurinsa irin wanda kake so ne saika karbi nasa.

Mutanen dake zaune a wannan gurin sunce suna matukar jin dadin wannan kasuwancin da suke.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here