Manyan yan Kannywood da suka hada da Adam Abdullahi Adam wanda aka fi sani da Daddy Hikima, Aminu Ala da Naziru Dan Hajiya sun shiga takarar siyasa a zaben 2023.
Jaruman fim din za su yi takara ne a karkashin jam’iyyar Action Democratic Party (ADP) wanda a cikinta ne tsohon hadimin shugaban kasa, Sha’aban Ibrahim Sharada ke neman takarar gwamna.
Sharada dai ya ayyana kudirinsa na neman kujerar gwamna karkashin ADP ne a ranar Lahadi 4 ga watan Satumba a wani taro da aka gudanar a cibiyar matasa ta Sani Abacha da ke Kano.
1. Daddy Hikima
Jarumi Adam Abdullahi Adam wanda aka fi sani da Daddy Hikima yana neman takarar kujerar dan majalisa mai wakiltan mazabar Kumbotso a karkashin jam’iyyar ADP.
Koda dai mutane da dama na sukar yadda yake fitowa a matsayin dan daba a fina-finai, Abale wanda ya kasance haifaffen dan karamar hukumar Kumbotso na daya daga cikin jaruman da ake yawan magana kansu a masana’antar.
Ya fito a fina-finai da dama kamar su A duniya, Haram, Iyyali Na, Labarina, Farin Wata, Na Ladidi, Sanda da sauransu.
2. Aminu Ladan Abubakar (Ala)
Aminu Ladan Abubakar wanda aka fi sani da Alan waka yana neman takarar dan majalisa mai wakiltan mazabar Nasarawa a majalisar tarayya.
Ala wanda ya kasance haifaffen Yakasai, birnin Kano, yayi fice sosai a duniyar mawakan Hausa kuma ya rubuta litattafai da dama da suka hada da Cin Zarafi, Bakar Aniya, Sawaba, Cin Fuska, Jirwaye, Tarzoma.
Mawakin ya yi karatu a jami’o’i da dama a ciki da wajen Najeriya.
3. Nazir Dan Hajiya
Shahararren furodusa, Naziru Dan Hajiya na neman takarar kujerar dan majalisar tarayya mai wakiltan mazabar Kura/Garun Malam.
Jarumin wanda aka haifa a garin Jos, jihar Filato, ya jagoranci shirya fina-finai kimanin guda 20 zuwa 30 da suka hada Bahaushiya, Baya da Kura, Gamdakatar, Halisa, Hijira, Al’ajabi, da sauransu.
Majiya: legit hausa