Sashen Ci gaban al’umma na masu yiwa kasa hidima sun kaddamar da wani allon gefen titi wanda yake dauke da sakonnin yaki da cin hanci da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa.

An kaddamar da allon ne a titin kasuwar Opolo dake, Yenogoa, jihar Bayelsa State.
Shugaban masu yiwa kasa hidimar Busayo Adepoju ya bayyana cewa sun yi haka ne don wayar da kan alúmma akan yaki da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa .
Akwai sakonni daban da aka rubuta a jikin allon dake kiran al’umma akan kauracewa cin hanci da rashawa, da kwarmata masu yin haka.