Kwamandan kungiyar tsaro ta vigilante a Jihar Kano, Shehu Rabi’u yace su na ɗaukar mata aiki, domin a kwai rawar da su ke taka wa a wajen tsaron jihar.
Da ya ke zanta wa da manema labarai a ofishinsa a Kano a yau Talata, Rabi’u ya ce ba ko wacce irin mace su ke ɗauka aikin tsaro ba, sai wacce ta dace.
Yace suna daukan ma’aikata aiki wadanda shekarun su su ka fara daga 18 zuwa 40, inda ya ƙara da cewa su na yin duba na tsanaki kafin ɗaukar ma’aikata domin guje wa daukar bara-gurbi cikin al’umma.
“Mukan ɗauki mata aiki na vigilante sabo da suma akwai rawar da suke takawa wajen magance aiyukan bata-gari, amma fa mu na ɗaukar mata ne da yardar iyayensu ko mijinsu ko wani shaƙiƙi nasu, don gudun yin kitso da kwarkwata”. Inji Shehu Rabi’u
Yace zuwa yanzu an samu ci gaban mai tarin yawa a fadin jihar Kano ta fuskar tsaro, kuma hakan na da alaka da irin yadda jami’an kungiyar vigilante ke gudanar da aikinsu ba dare ba rana domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
” Duk lokacin da kake tafiya cikin dare zaka ga jami’an suna zagayawa cikin unguwanni a tsakiyar dare, wannan ya kara taimakawa wajen inganta tsaro, Inda harkokin kwacen waya suka takaita sosai a jihar kano “. Inji Kwamandan
Yace akwai kyakyawar alakar aiki tsakanin su da sauran hukumomin tsaro dake Kano, musamman ƴan sanda, sabo da su suke kaiwa masu laifi idan sun kama don yin bincike tare da tura su kotu domin girbar abinda su ka shuka.
Majiya: daily Nigerian hausa