Wasu alamomi guda 4 da mace zata gane saurayi bata mata lokaci kawai yake ba aurarta yake so yayi ba.

0

Lokaci da dama samari suna zuwa gun yan mata kawai domin su yaudaresu ko kuma su bata musu lokaci ba tare da sun aure su ba.

 

Wasu za suje da manufofi da yawa gurin yan mata amma sai su fake da cewar sunzo ne kawai suyi soyayyar aure wanda daga karshe kuma sai su ware bayan sun bata was yarinya lokaci.

 

To yau zamu bayyana muku wasu alamomi wanda mace zata gane cewar saurayi bata mata lokaci kawai yake.

 

1. Rashin Gaskiya: Duk saurayinda zaizo gurinki amma yake boye miki wasu abubuwa nasa baya so ki sani kamar gidansu ko yan uwansa da sauransu.

 

2. Rashin kulawa: Duk saurayinda baya baki kulawa sosai a soyayyarku dashi ina baki shawara ki barshi kawai domin a karshen maganar barinki zaiyi koda a gaba domin duk wacce ba’a bata kulawa ba’a sonta.

See also  Wasu sabbin tuhume-tuhume da gwamnatin tarayya zata yiwa Emefiele

 

3. Neman yayi tarayya dake: Duk budurwar da saurayinta ya nemi ya kwanta da ita da niyyar cewa shine zai aureta to ba gaskiya bane domin bata ta kawai zaiyi ya wuce ba tare da ya aure ta ba domin duk saurayin da ya kusanci budurwa kafin aure to da wuya ya aure ta.

 

4. Kin shigo da maganar manya a lamarin soyayyar ku, duk lokacinda soyayya takai soyayya amma daga zarar anyi maganar ya turo manya sai yana zamewa to wannan ma ba aure bane a gabansa.

 

Allah yasa mu dace amin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here