Wata Gada Ta Rufta Da Jami’an Gwamnati Yayin Bikin Kaddamar da ita

0

Hankula sun tashi bayan wani karamin gada tsallakawa da kafa ya rufta a lokacin bikin kaddamar da shi a Jamhuriyar Demokradiyya ta Congo, (DRC).

 

Yan siyasa na Africa sun yi kaurin suna wurin yin manyan bukukuwa yayin kaddamar da ayyuka da suka yi.

 

A shekarar 2018, tsohon ministan kudi na Zimbabewa Patrick Chinamasa ya kaddamar da kwandon zuba shara kuma labarin ya bazu sosai a lokacin.

 

Wannan karon, yan siyasa ne daga kasar ta DRC suka so kaddamar da karamar gada na takawa da kafa, sai dai abubuwa ba su tafi yadda aka tsara ba.

 

Jami’an gwamnati sun taru don bikin. An gina karamin gadan ne don taimaka wa mutane tsallaka rafi a lokacin damina, don ruwa na shanye tsohuwar gadar.

 

Wasu mutane sun hau kan gadar, wanda fadinsa bai wuce mita biyu ba. A karshensa, an lika ribon mai launin ja, da ake sa ran daya cikin jami’an zai yanka da almakashi.

 

Kamar yadda bidiyon ya nuna, a lokacin da suke kan gadar, wasu tawagar mutanen suna kasa suna kalon bikin kaddamarwar.

Majiya: legit hausa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here