An kama budurwa bisa zargin kashe mahaifiyar saurayinta da adda

0

Hukumomi a Kamaru na zargin wata budurwa da hannu a kashe mahaifiyar saurayinta.

 

Lamarin ya faru ne a jiya Litinin a garin Fongo-Ndeng da ke yammacin kasar.

 

BBC ta rawaito cewa budurwar, Mabel, ta kashe matar, Ma’a Cecilia, mai shekara 64, ne ta hanyar sare mata wuya da adda.

 

Dattijuwar dai ita ce take nema wa danta auren budurwar, inda kafin a shirya komai, ta dauko ta ta kai ta gidanta suna zaune tare.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here