Muazu hassan
@ katsina city news
A jiya talata 6 /9/2022 mugun dan ta addar na dake da kyakykawar alaka da kariya ga gwamnatin zamfara ya kawo hari cikin jahar katsina.
Dan ta addar mai suna Dankarami Wanda yanzu yake watayawa shi da yaran shi a fadin jahar zamfara a tsanake.
Dankarami ya baro, sansaninshi dake zamfara da mayakanshi,ya kai hari a yankin Kankara.
Sojan sama, sun kai daukin gaggawa, Wanda ya jawo Dankarami, suka janye kuma suka rabu kashi kashi don komawa masaukinsu a zamfara
Wani gungun ne suna Kan hanyarsu ta komawa.suka kashe wasu sojoji biyu a yankin Danmusa.
Duk wani Hari mai muni a jahar katsina daga yankin zamfara ake shirya shi.
Hatta harin da ya tarwatsa wata motar sulke a yankin shimfida ta karamar hukumar jibia.maharan suna gama ta asarsu, zamfara suka shiga.
Dankarami shine Wanda majiyarmu ta tabbatar da cewa yana kitsa kawo Hari babban birnin katsina don ya firgita garin.
Bamu da wani tabbacin, ko gwamnatin zamfara na tsawata ma wadannan sojan bante nata.
Wadanda ake zargin ana sulhuntawa dasu, domin tanadin zaben 2023.
Katsina city news
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
Www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
Www.thelinksnews.com
07043777779 08137777245