Kabilar da Amarya ke kwana da surukinta a daren aure.

0

Duniya tana da matukar yawa tare da girma wannan yasa ake samun yankuna mabanbanta wanda suma suke da matukar yawa kuma suke da girma.

Yankin Africa yanki ne mai girman gaske a cikin duniya wanda yake da tarin mutane masu kabilu da yawa.

Yawan kabilun da nahiyar ke dasu yasa aka samu al’adu masu yawa, wasu abinda suke aikatawa a cikin al’adar tasu ko kadan babu dadi idan mutum ya gani ko kuma yaji.

Domin suna gabatar da abubuwa ne da ko kadan basu dace ba, to amma dake ance kowacce kabila tanada al’adunta abin bazai bawa mutane mamaki ba idan yaji yadda wasu kabilun ke gabatar da al’adunsu.

Yau cikin shirin namu muna tafe muku ne da sunan wata kabila mai abin mamaki, wacce dole sai sabuwar amarya ta kwanta da mahaifin ango domin gwada budurcinta

See also  ME YA FARU NE. A ZIYARAR SHUGABAN KASA BUHARI KATSINA?

Kabilar kalanga ko kuma bakalanga kabila ce dake can zaune a wani bangare na arewacin kasar Botswana da kuma yammaci da kudancin kasar Zimbabwe.

Mafi yawancinsu suna zaune ne a guraren da suka gina da itatuwa da kuma ganyen bishiyoyi, sannan kayan da suke sanyawa sunfi sanya kaya na namun dabbobi.

Kabilar kalanga suna da wani tsari idan suka zo bikin aurensu inda dole yarinyar da za’a aurar sai ta kwanta da mahaifin mijin data aura domin ya tabbatar da cikar budurcinta.

Sannan mutanen dake cikin wannan kabilar sun shaida cewar auren yafi dadi idan akai hakan kuma anfi zaman lafiya tare da mutunta juna a tsakani.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here