Wata mahaifiya yar kasar Indiya ta yi fada da wata damisa da hannunta don ceton jaririn ta.

0

Matar Mai Suna Archana Choudhary ta fice daga gidanta da ke jihar Madhya Pradesh da ke tsakiyar kasar india a ranar Lahadi da daddare

 

Damisar ta kubce daga inda take a Tsare ta afka musu, kamar yadda wani jami’in yankin Sanjeev Shrivastava ya shaida wa AFP.

 

damisar ta kai hari da niyar cinye jaririn amma mahaifiyar ta yi kukari ta ceto shi

 

Damisar ta yi ta kokarin kwace yaron har mutanen kauyen suka ji kukan ta suka garzaya domin ceton ta.

 

Damisar ta ruga cikin daji bayan da mutanen kauyen suka karasu wajen su.

 

Yanzu dai an kwantar da ita matar a asibiti, Jaririn nata kuma yana jin sauki sosai Kamar yadda Shrivastava ya shaida.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here