Rahotanni daga jihar Kogin Najeriya na cewa ‘yan fashi da makamai sun far wa rassan bankunann Zenith, da UBA da First Bank da ke karamar hukumar Ankpa.
BBC ta rawaito cewa lamarin ya faru da tsakar rana, inda ɓarayin suka yi awon-gaba da makudan kudaden da ba a san adadinsu ba.
Ganau sun shaidawa jaridar Daily Trust cewa, ‘yan fashin sun zo bankunan cikin kananan motoci da babura da bas-bas, inda suka wawushe kudin da ke bankunan da wurin hada-hadar kasuwancin kudi na POS da ke kusa da bankunan.
‘Yan bindigan sun yi ta harbi kan mai uwa da wabi kafin su tsere ba tare da kama ko guda daya daga cikin su ba, sun kuma shafe sa’o’i su na gudanar da aikin.
Wani mazaunin kusa da inda lamarin ya faru, ya shaidawa Daily Trust cewa mutane sun shiga gida lokacin da suka fara harbin kan mai tsautsayi.
Kuma jami’an tsaro ba su isa wajen ba har sai bayan sun gama cin karensu ba babbaka.