ABIN ALHERI: Gwamna Buni ya baiwa iyalan Sheikh Aisami da soja ya kashe kyautar gidaje

0

Gwamnan Jihar Yobe Mai Mala Buni, a jiya Laraba ya raba wa iyalin marigayi Sheikh Goni Aisami kyautar gidaje.

 

Mai ba wa gwamnan shawara na musamman kan harkokin addini, Ustaz BG Kyari ne ya gabatar da kyautar a gaban Sarkin Bade, Alhaji Abubakar Umar Sulyman.

 

Daily Nigerian Hausa ta jiyo cewa an baiwa matan marigayin kowacce gida, da su ka haɗa da Aisha Badamasi da kuma Hajara Muhammad Ibrahim.

 

Sannan gwamnan ya baiwa ƴaƴan marigayin su uku, waɗanda mahaifiyarsu ba ta gidan gida guda ɗaya.

 

Dukkanin gidajen da aka saya suna unguwar Yusufari bypass, unguwar Isari a garin Gashua, a Ƙaramar Hukumar Bade ta jihar Yobe, inda kuma an gabatar da takardu.

See also  Hajji 2023: Tinubu Ya Bukaci Alhazai Da Su Kara Hakuri Da Halin Matsi Da Takura Da Suke Ciki

 

A nasa jawabin, Mai Martaba Sarkin Bade, HRH Alhaji Abubakar Umar Sulaiman ya yaba da kokarin mai girma gwamna a kodayaushe na tallafin gaggawa da kuma tallafawa al’ummar jihar ta bangarori da dama.

Majiya: daily Nigerian hausa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here