BOKO HARAM NA RIKE DA KAFTIN DIN SOJA A KATSINA?

0

Muazu Hassan

@ katsina city news

 

A ranar 30/8/2022.wasu sojaji suna Kan hanyarsu ta Rakiyar wasu mutane daga Gurbi zuwa Garin Shimfida, Bam da aka binne a Kan hanya ya tashi a kasan watan motar sulke ta APC wadda sojoji ke a ciki.

Rahotonni sunce, wasu sojoji sun mutu wasu kuma suka ji mummunan Rauni wadanda aka kawo su asibiti a katsina .

Rahatanni sun ce soja biyu sun bace, cikinsu har da mai mukamin kamftin Wanda ake Kira da suna Musa Amadu.

Anyi ta Rade Radin kaftin Musa yana da Rai ko ya mutu.ko kuma yaji ciwo yana amsar magani.

Jaridun katsina city news sun tabbatar daga Majiyoyin soja da kuma ta jami an tsaro cewa, kaftin Musa yana da rai yana a hannun yan ta addar da suka dasa Bam din sune kuma suka kama shi da rai.

Majiyarmu tace kamfin Musa yayi magana da makusantar shi daga inda yan ta addar ke tsare dashi.

Majiyarmu tace yan ta addar sun saka kudin fansa akan shi kamar yadda wani makusancinsa ya tabbatar ma jaridun mu.

See also  ƳAN BINDIGA SUN BUƊE MA MOTAR ƳAN KASUWA WUTA A BATSARI

Suwa suka kai harin? Binciken mu, a kauyukan da abin ya faru sun tabbatar wasu mahara ne da suka zo daga dajin zamfara.

Ganau sun ce Maharan sun fi kama da yan Boko haram.wadanda ke samun rakiyar fulani barayin daji.

Ganau sunce maharan sun gargadi mutanen kauyukan ba ruwansu da abin da ya kawo su.inda suka dasa Bam suka kuma tsara tashi dai dai isowar motar sulken soja ta APC.

Dajin Jahar zamfara nan ne babbar Mafakan duk yan ta addar dake addabar jahar katsina.suna samon masauki a can da sunan sasanci.

Munyi kokarin jin ta bakin mai magana da yawun soja na kasa,amma wayar sa bata tafiya.mun aika masa da sakon rubutu na waya,har zuwa rubuta rahoton nan babu amsa.

Katsina city news

Www.katsinacitynews.com

Jaridar taskar labarai

Www.jaridartaskarlabarai.com

The links news

Www.thelinksnews.com

07043777779 08137777246

Email:katsinacitynews2@gmail.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here