Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, wani wa da kani sun guntule hannun mahaifinsu dan shekara 60 don kawai su samu damar sace shanunsa.
‘Yan uwan biyu da aka ce makiyaya ne, sune Bello Usman da Shehu Abubakar, kuma sun hada baki ne da wasu mutane biyu domin aikata wannan mummunan barna.
Hukumar binciken manyan laifuka ta kasa (SCIID) ta gurfanar da su a gaban kotu bisa tuhumarsa laifuka biyu da suka hada da hada baki da kuma aikata ta’addanci mai cutarwa.
Shehu sa Bello, wadanda suka amsa aikata laifinsu, sun ce sun yi kokarin sace shanun mahaifin nasu ne amma ya kawo musu cikas, daga suka ce basu da zabnin da ya wuce su sare hannunsa.
A ganin da manima labarai suka yi, sun ce an datse hannu daya na dattijon gaba dayansa yayin da dayan kuma ya kusa gutsurewa sai aka daure shi bandeji, BrainNews ta tattaro.
Sauran mutanen biyu da ake zargin sun aikata laifin tare sun tsere, sai dai an gayyato iyalansu, kuma an nemi su nemo su duk inda suka shiga nan da ranar da kotu za ta sake zama.
Alkalin kotun Minna, Fati Hassan Umar, ta ba da umarnin ci gaba da tsare tsagerun a hannun ‘yan sanda har zuwa ranar 26 ga watan Satumba.
Rahoton ya ce, an garzayo da dattijon ne kotu daga asibitin da yake jinya.
Majiya: legit hausa