Labarin Wani sarki da ya auri mata 70 a kasar Swaziland

0

Kunsan kowa daga cikin mutane nada muradi da ra’ayin kansa musamman idan ya samu kudi ko kuma mulki, za kuga ya kirkiro wani abu da yake ganin shi a gurinsa daidai ne yace zai aikata ko domin ya kafa tarihi ma.

Hakan yasa wasu masu kudin suke gabatar da wasu abubuwa na ban mamaki, to yau cikin shirin namu muna tafe muku ne da labarin wani sarki a kasar Swaziland daya auri mata 70 rigis shi kadai.

Sarkin mai suna Sobhuza na biyu shine sarkin daya auri mata har guda 70 kuma yake zaman aure dasu ba tare da wata damuwa a gareshi ba, wanda su kuma suka haifa masa yaya har kimanin 210.

See also  Girman Zunubin Buhari Ya Fi Karfin A Yafe Masa Inji IPOB

Bincike ya nuna cewar sarki Sobhuza yana da jikoki a kalla dubu daya zuwa sama.

Sarki Sobhuza ya jima akan karagar mulki wannan ya bashi damar yin abubuwa da dama wanda ransa yake so a wancan lokacin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here