SHUGABA BUHARI YAYI JIMAMIN RASUWAN SARAUNIYAR INGILA

0

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari yaji baƙin ciki matukar gaske da samun labarin Rasuwar Sarauniyar Elizabeth na biyu na Ƙasar Birtaniya.

 

“Ni da iyalai na, da Al’umman Najeriya sama da Miliyan Ɗari Biyu, sun ji ɓacin Rai matuka-gaya na Rasuwar Sarauniya Elizabeth, wanda hakan ya kawo ƙarshen Mulki ta na tsawon shekaru Saba’in mai cike da abin sha’awa da babu irin sa. Mulkin Marigayiyar shine kadai Masarauta mai Girma a Turai da kashi Chas’in cikin Ɗari na Al’umman mu suka sani.

 

A daidai wannan lokaci na jimami munbi sahun sauran kasashen Duniya gurin jimamin rashin Sarauniya Elizabeth. “Muna tare da nuna Alhinin mu ga Ilahirin iyalan Masarautan da Mutanen Ƙasar Birtaniya dama daukacin ƙasashe Rainron Ingila na (Commonwealth).

 

Tarihin Najeriya a matsayin Ƙasa bazai taɓa kammaluwa ba, ba tare da an tabo babin Sarauniya Elizabeth na biyu ba, dogon Alakanta da Duniya Shugaba ce da tayi fice. Ta sa daukar da Rayuwar ta Gurin gina Ƙasar ta da Ƙasashe Rainon Ingila dama kokarin tabbatar da Duniya dukka ta zamo guri mai kyau”.

 

Shugaba Buhari yayi Maraba da Mai Girma Yarima Charles bisa Gadon Mulki da yayi wanda hakan na daidai da tsarin Masarautan, ya kuma yi Addu’an ganin ci gaba da samun karin ingantuwar Dangantaka da alaka tsakanin kasashen biyu a yayin mulkin Yarima Charles na Uku.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here