Duk Karyace Muke Yiwa Mutane, Auren Mace Fiye Da Daya Halas Ne: Rabaran Fada.

0

Wani babban Bishop na cocin Anglican dake Nnewi jihar Anambra, Rabaran Fada Ogbuchukwu Lotanna, ya yi murabus daga kujerarsa a Cocin.

 

Rabaran Fada Lotanna, a jawabin murabus dinsa yace ya samu sabon umurni na ya kwadaitar da mutane kan auren mace fiye da daya don a rage zinace-zinace cikin al’umma, rahoton Punch.

 

A cewarsa, auren mace fiye da guda ba haramun bane sabanin abinda ake tunani.

 

Yace Ubangiji na son mutane su auri mata fiye da daya maimakon neman matan aure da yan mata. Yace Coci ta dade tana boye hakan ga mambobinta kuma lokaci ya yi da za’a fadawa mutane gaskiya.

See also  FG gives interest-free loan to 98,000 beneficiaries

 

Ya yi kira ga Maza su auri ‘yan matan da suke lalata dasu don kada su shiga wuta rana gobe Kiyama, Kamar yadda TheNation ta Ruwaito.

 

majiya: legit hausa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here