Rahotanni sun kawo cewa kasar Amurka na neman wani matashi dan Najeriya, Chidozie Collins Obasi, mai shekaru 29 ruwa a jallo kan zargin zambar kudade.
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa ana zargin dan Najeriyan da damfarar asibitocin Amurka kudi har dala miliyan 31 ta hanyar tallata na’urorin hura iska na korona wadanda babu su.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga sashin shari’a na Amurka a ranar Juma’a, 9 ga watan Satumba.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa wanda ake zargin ya aikata wannan ta’asar ne daga Najeriya da taimakon abokan harkallarsa na kasar waje a tsakanin Satumban 2018 da Yunin 2020.
Ana zargin Obasi da sauran abokan damfararsa sun samu fiye da $31,000,000 ta wannan hanya, inda yawancin kudaden suka fito daga jihar New York.
majiya: legit hausa