Tarihin Sarki Attah Wanda Ya Zaɓi Ya Kashe Kansa Maimakon Ya Rusuna Wa Sarauniyar Ingila

0

Daga Aliyu Adamu Tsiga

 

Attah Ameh Oboni ya kasance Sarkin Igala da ake girmamawa. A wani taro na musamman da aka yi a Kaduna wanda ya ƙunshi manyan sarakunan gargajiya a Najeriya, kuma sarauniyar Ingila ta halarci taron, an buƙaci Attah Ameh da ya cire hular sa domin gaishe da Sarauniyar Ingila kamar yadda wasu suka yi. Ko da yake ya ƙi har sai da suka ce toh ya bar wurin taron idan ba zai cire hularsa ba kamar yadda sauran sarakuna sukayi.

 

Attah ya cire hularsa a cikin jama’a. Gaba ɗayan zauren da suka sauka ya mamaye da ƙudan zuma wanda ya fito daga hular Attah Ameh Oboni da ya cire domin ya gaida Sarauniya.

 

Sarauniyar Ingila da sauran masu mulki a taron sun yi gudun hijira sai dai Oba na Benin, abokin hamayyarsa wanda Attah Ameh ya buƙaci ya fita kafin ya cire hularsa. Zauren ya zama babu kowa a yayin da wasu ƙudan zuma suka yi ta shawagi a cikin wurin da ake taron har aka kammala taron.

 

Kamar yadda tarihi ya nuna, an buƙaci jami’an tsaro da su kama Attah Ameh Oboni, tare da ɗaura masa mari, bayan sunyi hakan, amma sarƙar ta faɗo daga hannunsa.

 

Daga baya sai aka kulle shi a ɗaki bisa umarnin sarakunan Arewa kuma jami’an tsaro suka tsare shi amma daga baya jami’an suka gano cewa ya bar ɗakin.

 

Eh, lokacin da jami’an tsaro suka kai shi a kulle, sai ya ce wa direbansa Amanabo mai albarka, ya ɗauki mota ya nufi Idah, sai jami’an tsaro suka kulle shi a ɗaki.

 

Sannan ya gargaɗi Amanabo da kada ya waiwaya har sai ya ji sanyin iska a cikin motar. Ko da yake Amanabo ya ɗan yi jayayya cewa ba zai iya barin Attah a can ba amma daga baya ya yi biyayya ya fara tuƙi ya koma Idah daga Kaduna. Bayan wani lokaci sai ya ji sanyin iska a cikin motar, Attah Ameh na zaune a cikin motar.

 

Lamarin da ya faru a taron ya sa sarakunan gargajiya da dama waɗanda galibinsu ƴan Arewa ne suka fusata musamman sanya sarakuna su yi takara a haka saboda ƙudan zuma. Wannan ya zama zunubi ɗaya mai muhimmanci, kuma ya kasance kamar “zunubi ɗaya ya yi yawa”.

 

Ita ma sarauniyar Englnad ba ta ji daɗi ba, sai su (Sarauniya da shugabannin arewa) suka fara neman hanyar da za a cire Attah Ameh daga kan karagar mulki tunda ya ƙara tauri da rashin kamun kai, tare da neman wanda zai maye gurbinsa da kuma wanda zaiyi musu biyayya.

 

Igala na da bukukuwan al’adu daban-daban, ɗaya daga cikinsu shi ne Ocho. Ana bikin Ocho kafin a fara noma, kuma lokaci ne da Attah Igala ke addu’ar Allah Ya ba shi isasshen ruwan sama, domin ayi noma mai albarka, samun nasara a wurin farauta.

 

Ana yin bikin ne a daji kuma ana kiran wurin da Ere-ocho, inda Attah zai fara farauta har sai ya kashe Buffalo ko wata dabba mai ƙarfi.

 

Al’ummar Idah inda Ocho ke faruwa ana kiranta Ogo-Efa. Ya yi ɗan sadaukarwa ga kakanni ta hanyar amfani da tsuntsu a cikin wannan tsari, kuma wannan shi ne don gano ko za a sami albarka ko matsaloli a cikin ƙasa bayan bikin al’adar Ocho.

See also  Legas: An yanke wa makaneza hukuncin kisa bisa yi wa likita fashin Naira dubu 57

 

Kafin wannan lokacin, maƙiya na cikin gida (daga cikin mutanen Igala), musamman masu alaƙa da shugabannin yankin arewa, sun yi ta ƙoƙar wajen ganin an samu wata hujja ta gaskiya ko ta ƙarya wadda za a iya amfani da ita wajen tsige shi daga karagar mulki.

 

Jinin dabbar da aka yi amfani da ita a matsayin hadaya a filin Ocho yanzu ya zama abin da maƙiya za su yi amfani da shi a kansa. Waɗannan ƴan ƙabilar Igala biyu ne suka rubuta takarda zuwa ga Sarauniya da wasu shugabannin Arewa cewa Attah Ameh yana sadaukar da mutane a lokacin bukukuwan Ocho.

 

Da yake suna neman hanyar da za su raba shi da mulki ne, sai aka yanke hukuncin da ya kamata aka tsige shi, duk da ba a kammala bincike ba.

 

Bugu da ƙari, nan take aka dakatar da duk wasu bukukuwan al’adun Igala da suka haɗa da na Ocho wanda hakan ya kasance kusan shekaru 63 har sai da Gwamna Yahaya Bello ya cire su a bisa rokon Attah Igala na yanzu.

 

Tuni dai kafin wannan lokacin, Oba na Benin da ke da irin wannan rikici da turawan Ingila an riga an tsige shi, aka kore shi daga Benin. Don haka, Attah Ameh Oboni ya san cewa a wannan lokacin, ko ta wace hanya, za ta iya ɗage wannan muguwar ranar ne kawai domin maƙiyan sa ba za su taɓa yin kasa a gwiwa ba har sai sun kawar da shi.

 

Sakamakon samfurin jinin da aka ɗauko daga wurin Ocho da aka kai jami’ar Ibadan domin bincike ya iso inda aka tabbatar da cewa jinin dabba ne ba mutum ba. Amma abin baƙin ciki, Sarkin da ake girmamawa, Attah Ameh ya rasu kafin a kawo sakamakon.

 

Amma Attah Ameh, da yake yana da tabbacin cewa abokan gaban sa ne suka zarge shi ba bisa ƙa’ida ba, musamman ma ƴan ƙabilar Igala da suka rubuta takardar koke a kansa, wanda ke nuna farkon tsige shi daga karagar mulki, ya yi wasu maganganu kafin rasuwarsa.

 

An dai jiyo shi yana cewa “wanda ya rubuta masa takardar koke sai wannan hannun ya bushe, kuma za a binne shugaban ƙungiyar ko masu shigar da ƙara har sau uku”.

 

Yayin da hannun ya bushe kamar yadda ya faɗa, an binne ɗayan kamar yadda ya faɗa shima, na farko kafa, na biyu hannunsa, na uku kuma da kansa, duk an binne su a lokuta daban-daban a kuma wurare daban-daban.

 

Bugu da ƙari, an ba shi wannan bayanin na tsige shi ne a wani taro daga inda ya kamata ya koma Idah ya shirya barin gadon sarautar, ya tsaya kan wata hanya a ƙasar Igala da ake kira Dekina, a nan ne ya kashe kansa.

 

Kafin ya ɗauki ransa, an jiyo shi yana cewa garin Dekina zai yi farin jini amma ci gabansa ba zai kai matsayin shahararsa ba.

 

An kuma ruwaito cewa, saboda Igala shi ne asalin abin da ya faru da shi, za a samu rashin haɗin kai a tsakanin al’ummar Igala har zuwa lokacin mulkin jininsa (dansa) a matsayin Attah, kuma duk Igala ba tare da la’akari da inda suke ba za a sa ke haɗuwa.

Majiya: RARIYA

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here