ANYI ƊAUKI BA DAƊI TSAKANIN ƁARAYIN DAJI DA ƳAN SPECIAL HUNTERS (CIVILIAN JTF) A BATSARI

0

Misbahu Ahmad batsari

@ katsina city news

A ranar lahadi 11-09-2022 da misalin ƙarfe biyu na rana wasu gungun ƴan bindiga ɗauke da miyagun makamai suka afka ma unguwar katoge da tashar Ruma cikin garin Batsari, hedikwatar ƙaramar hukumar Batsari ta jihar Katsina.

 

Ƴan bindiga dake kan babura guda goma kowane ɗauke da goyo, sun shigo garin ta gefen makarantar jeka ka dawon ƴan mata ta al’umma, watau CGDSS Batsari, inda suka biyo ta titin tashar ruma suka suna harbi kan mai uwa da wabi, suka ɗauki babura guda biyar na mutane.

Suna cikin cin ganiyar su sai ga ƴan hunters a guje wasu ƙasa wasu kan babura suka tunkare su suna ƙarya kuke matsiyata, suna harbe-harbe kamar ana yaƙi al’ummar gari kuma suka jajirce akayi ta fafatawa, wanda yasa maharan suka juya a guje domin neman su tsira, dayawan su, sun zubar da baburansu sun rankaya a guje. Mun samu tabbacin an kashe ɗaya daga cikin ɓarayin suma ɓarayin sun harbi mutum ɗaya.

See also  An maido da waɗanda aka kora ba bisa ka'idaba a bakin aiki a jami'ar UMYU

 

An samu nasarar karɓe babura guda tara daga hannun ɓarayin waɗanda suka gudu suka bari, amma huɗu daga cikin baburan na mutanen gari ne da suka sata. Haka kuma wata majiya na nuni da cewa har bindigogi biyu, ƴan JTF suka ƙwato hannun ɓarayin.

Har zuwa fitar da rahoton nan, yan sanda basu fitar da sanarwa ba, akan wannan fafatawar.

Katsina city news

@ www.katsinacitynews.com

Jaridar taskar labarai

@ www.jaridartaskarlabarai.com

The links news

@ www.thelinksnews.com

07043777779 08137777245

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here