Yadda ƴan majalisar Shura ta Shekarau su ke raba Naira miliyan 100 da Atiku ya basu

0

Wasu hotuna sun nuna wasu mambobin Shura, majalisar shawara ta harkar siyasar Sanata Ibrahim Shekarau, suna raba wani kaso na Naira miliyan 100 da ake zargin ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya bayar domin tara magoya bayan jam’iyyar a ziyarar da ya kai Kano.

Wasu majiyoyi sun shaidawa DAILY NIGERIAN cewa ɗan takarar shugaban ƙasa ya yiwa shugabannin PDP na Kano wanka da kuɗi har naira miliyan 130, inda Malam Shekarau ya samu kaso mafi tsoka na Naira miliyan 100, shi kuma ɓangaren Aminu Wali ya samu Naira miliyan 30.

A karshen watan Agusta ke dai Atiku ya ziyarci Kano domin karɓar Malam Shekarau, wanda ya sauya sheƙa daga jam’iyyar NNPP ta Rabiu Kwankwaso zuwa PDP.

See also  FG earmarks N15bn for Katsina airport expansion – Aviation Minister


Daga shafin Facebook na daily nigeria

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here