An Yi Ruwan Kankara Zalla A Jahar Taraba

0

Jaridar Aminiya Ta Ruwaito cewa An yi ruwan kankara zalla a garin Nguroje da ke Karamar Hukumar Sardauna a tsaunin Mambilla na Jihar Taraba.

 

An yi ruwan ne a ranar Talata kuma an kwashe kimanin awa daya ana yin shi ba tare da saukan ruwa irin wanda aka saba gani ba.

 

Wani mazaunin garin na Nguroje mai suna Abdulrashid Jobbdi ya shaida wa Aminiya cewa wannan lamari ya bai wa mazauna garin mamaki.

 

A cewarsa, ba su taba samun ruwan na kankara zalla ba, sai dai akan sami saukar kankara a lokacin ruwan sama.

 

“Amma yau a maimakon ruwan sama, sai kankara zalla ta sauka,” a cewar Abdulrashid

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here