Mahaddacin Al-qur’anin Nan Da Aka Ƙwaƙulewa Idanu A Jihar Bauchi Sun Kai Wa Gwamnan Bauchi Ziyarar Godiya Shi Da Iyayensa

0

Daga Muhammad Aminu Kabir

 

Matashin nan mai suna Uzairu Salisu wanda aka ƙwalƙulewa idanu a jihar Bauchi ɗan asalin ƙaramar hukumar Bindawa ta jihar Katsina tare da iyayensa sun kai wa gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed ziyarar godiya.

Matashin da ibtila’in masu ƙwaƙule idanu ya faɗa wa wato Uzairu Salisu, ɗan yankin Ƴar Ya’u ne a Tama dake ƙaramar hukumar Bindawa ta jihar Katsina.

 

Uzairu matashi ne ɗan shekaru 18 kuma mahaddacin Al-qur’ani mai girma ne, neman karatu ne ya kai shi jihar Bauchi inda ya gamu da wannan ibtila’in.

 

Matashin shi da iyayensa sun kai ziyarar godiya zuwa gidan gwamnatin jihar Bauchi, bisa kula da shi da akayi yayin da yake neman lafiya bisa kulawar uwar gidan gwamnan jihar ta Bauchi.

See also  Ta Shayar Da Mahaifinta Ruwan Nononta Don Kar Ya Mutu

 

Idan dai ba’a manta ba lamarin ya faru ne a watan Yuni na wannan shekarar, inda jami’an tsaron ƴan sanda sukayi nasarar kama wanda yayi wannan aika-aikar mai suna Ezikel.

 

Kazalika a wancen lokacin matar gwamnan Bauchi ta ziyarci matashin, kuma tayi alƙawarin kula da shi tare kuma da shan alwashin cewa lallai gwamnatin jihar ba za ta bar wannan lamarin haka nan ba, za su tabbatar sai anyi wa wanda aka kama da laifin hukuncin da ya kamata.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here