Mataimakin shugaban ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya sauka a Nairobi babban birnin ƙasar Kenya domin halartar bikin rantsar da sabon Shugaban kasar William Ruto.
Mataimakin shugaban ƙasan dai ya sauka ne a filin jiragin sama na Jomo Kenyatta, inda ya samu tarbar tsohon gwamnan yankin Kwale, Salim Mvurya da jakadan Najeriya a ƙasar, Yusuf Yumusa da sauran manyan jami’an gwamnati.
Tun a ranar 15 ga watan jiya na Agusta ne hukumar zaben ƙasar ta Kenya ta sanar da sunan mataimakin shugaban ƙasar, Ruto a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasar, wanda aka yi a ranar 9 ga watan na Agusta.
Haka kuma ta ƙara da cewa, Farfesa Yemi Osinbajo ya samu rakiyar karamin ministan harkokin waje, Ambasada Zubairu Dada da mai bai wa shugaban ƙasa shawara akan harkokin siyasa, Sanata Babafemi Ojudu.