Hon. Aminu Chindo Ya Samarda Fitilun Solar Dari A Karamar Hukumar Katsina.

0

A ranar 14/9/2022 ne Aka Kaddamar Da Bada Gudummuwar Fitilu Masu Anfani da hasken Rana Wato solar a karamar hukumar katsina.

Fitilun Wanda Dan Takarar Kujerar Majalisa ta Tarayya a karkashin Jam’iyyar PDP Hon. Aminu Chindo (Sadaukin Katsina) ya samarwa kowace mazaba a karamar hukumar Katsina.

 

Fitilun Zasu samar da yanayin da zai bada dama Mutane su iya lura da shige da ficen bakuwar Fuska a cikin Unguwannin Birnin Katsina, musamman da daddare, domin inganta tsaro.

Hon. Cindo ya bayyana aniyar sa ta cigaba da wadata garin Katsina da wannan Lantarki na Sola, inda yace da yardar Allah ko ina a cikin Mazabar Katsina Gudummuwar hasken zai shiga, amma yanzu za’a fara badawa a yankunan mazabu na cikin Birni.

See also  An Kaddamar da kwamitin yakin neman zaben Dan Takarar Gwamnan jihar Katsina da Mataimakin sa a Karkashin Jam'iyyar Accord.

 

Hon. Chindo da ya samu wakilcin Alhaji Shehu Kofar Sauri, kuma Shugaban Elders na karamar hukumar Katsina, ya bayyana Aikin sanya Fitilun zai kasance a karkashin jagorancin Uwar jam’iyyar PDP da Ciyaman da Kansilolinshi.

An gudanar da taron bisa jagorancin shugaban jam’iyyar PDP na karamar hukumar Katsina da dukkanin Kansiloli goma sha biyu dake karamar hukumar da shugabannin jam’iyyar PDP na mazabu (Ward) a gidan Ɗantakarar Hon. Aminu Chindo dake Bayan gidan Dikko Inde a cikin birnin Katsina.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here