Wata gagarumar ruwan kankara ya lalata gonaki da gidajen jama’a a yankunan Dutsen-Kura/Kanya da Gozaki a karamar hukumar Kafur ta jihar Katsina.
Malam Abdullahi Gozaki, wani mazaunin garin Gozaki ya sanar da Daily Trust cewa babu wani mutum daya da ya taba fuskantar irin wannan lamarin a yankin
Yace gonakinsu, rufin gidaje da gilasan motoci duk suna lalace sakamakon ruwan kankarar da aka yi na tsawon mintuna
Ya jero yankunan da lamarin ya shafa kamar haka: Gidan Danwada, Gidan Sabo, Kabalawa, Unguwar Tsamiya, Dandabo, Unguwar Maigarma, Uguwar Wanzamai da Unguwar Fulani
A yayin tsokaci kan faruwar lamarin, shugaban karamar hukumar Kafur, Alhaji garba Kanya, yace kankarar ta lalata sama da gonaki 300 a yankuna da dama
Ya kara da cewa, hukumomin da suka dace daga ciki akwai Hukumar kula da aikin noma da raya karkara, KTARDA da hukumar kula da tallafiin gaggawa, SEMA, duk an sanar da su yawan barnar
majiya: legit hausa . . . . . legit hausa