Yan Sanda Sun Kama Amarya Kan Laifin Sata A Wajen Bikinta

0

Hukumomin ’yan sandan kasar Uganda suna tuhumar wasu jami’ansu hudu da laifin kama wata amarya a wajen biki inda suke zarginta da laifin sata.

 

Kakakin rundunar, Mista Fred Enanga, ya ce ana tuhumar ’yan sandan da yin abin da bai dace ba, lamarin da ake ganin zai sa su iya rasa aikinsu.

 

Yan sandan sun kama amaryar ce ana tsakiyar bikinta a ranar Asabar da daddare inda suka kai ta ofishinsu da ke garin Mbararata, a yammacin kasar Uganda ta kuma shafe daren a tsare sai washegari da safe aka sake ta.

 

Rundunar ’Yan sandan kasar ta ce jami’an nasu sun kama amaryar ce ba tare da kwakkwarar hujja ba.

 

Mista Enanga ya ce lamarin sam bai yi dadi ba, domin ga amaryar ranar farin cikinta ya zame mata ranar bakin ciki.

 

Dan sandan ya ce yanzu haka an kama daya daga cikin ’yan sandan da suka aikata wannan rashin kirki, sauran ukun kuma sun buya inda ake neman su ruwa a jallo.

 

Shugaban wurin da amaryar ta yi aiki a baya ne ya zarge ta da sata, shi ya sa ya fada wa ’yan sandan hudu su kuma suka dira wajen bikin tare da yin awon gaba da ita.

Majiya: aminiya

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here