”YAN TA’ ADDA, YARAN ALERU SUN NUFO KATSINA?

0

@ katsina city news

Majiyoyi masu karfin gaske dake da alaka jami “an tsaro masu Sanya ido da tattara bayanai akan masu aikata, miyagun laifuffuka sun tabbatar ma da jaridun katsina city news,cewa anga wasu Babura kamar guda arba in sun baro Dutsen sola garin shararren Dan ta addar nan mai suna Adamu Aleru.sun tunkaro jahar katsina.

Wasu kauyukan da masu Baburan suka bi, wani ‘Dan sa kai ya tabbatar ma da jaridun mu cewa sun Kirga Babura 40 kowane Babur da goyon daya daya.

Wata majiya tace, sun rika haduwa da wasu Baburan akan hanya suna hadewa dasu.

Majiyarmu tace, yaran Aleru sun fita daga dajin zamfara ya zuwa lokacin wannan rahoton suna cikin dajin jahar katsina.

See also  An Ɗirka Ma Wani Matashi Bindiga Har Lahira A Wurin Gwajin Maganin Bindiga

Majiyarmu tace, Babu Wanda yasan ina zasu kai Kari? Ko kuma ina suka dosa?

Adamu aleru, shine Wanda aka ba sarkin fulanin daji a jahar zamfara,kuma yana da kyakykawar alaka ta sulhu da gwamnatin jahar zamfara.

Wadannan miyagun ko ina suka dosa? Ko ina zasu kai Hari? Allah yayi maganin su.

Katsina city news

Www.katsinacitynews.com

Jaridar taskar labarai

Www.jaridartaskarlabarai.com

The links news

Www.thelinksnews.com

07043777779 08137777245

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here