An Gano Masallacin Da Ya Shekara 37 A Cikin Ruwa Bai Rushe Ba

0

Kamar yadda Jaridar Aminiya Ta Ruwaito cewa Wani masallaci ya bayyana, shekara 37 bayan nitsewarsa cikin wata madatsar ruwa da ke kasar Indiya

 

Masallacin, wanda ake yi masa lakabi da Masjid Noori ya nitse ne a madatsar ruwar Phulwaria da ke jihar Bihar a shekarar 1985 yanzu kuma da ruwan ya janye sai ya ga shi ya bayyana bai rushe ba.

 

Mutanen yankin sun ce masallacin ya dade a wurin kafin a soma ginin madatsar ruwar, wanda hakan ta sa aka kwashe mutanen yankin tare da matsar da su zuwa wani wuri a 1979.

 

Bayan tashin jama’a an bar masallacin a yashe, a inda bayan gama aikin madatsar ruwar, ruwa ya mamaye yankin baki daya har ya shanye kan masallacin a inda nutse ba a ganin ko alamarsa.

See also  Atiku Ya Bukaci Yin Sabuwar Maja Domin Tunkarar Jam'iyyar APC

 

Karancin ruwa da kuma fari da ake fama da shi a yankin a yanzu haka, ta sa madatsar ruwan ta kafe.

 

Wannan ya sa masallacin ya bayyana, kuma a tsaye kamar yadda yake a da, bai kuma rushe ba.

 

Bayyanar masallacin ta sa mutane na ta tururuwa cikin tabo da laka zuwa ganinsa suna kuma shiga cikinsa.

 

An kiyasta shekarun ginin masallacin 120 a duniya la’akari da tsari da kuma yanayin gininsa, a cewar masana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here