Dan Majalisar tarayya mai wakiltar karamar hukumar Katsina ya kaddamar Da Gyaran Asibitin Kambarawa

0

Daga Muhammad Kabir

 

A kukarinsa na inganta jindadin al’ummar sa Dan Majalisa Mai wakiltar Karamar Hukumar katsina a Majalisar wakilai ta Tarayya Hon. Salisu iro isansi ya kaddamar da Gyaran Asibiti Dake bayan Hajji Camp A ranar 15/9/2022.

Dayake magana a madadin Hon. isansi Alh. Umar Darma Yace Akwai Aikace-aikace da dama da Mutane Zasu Amfana daga cikin ayyukan Akwai Asibitin da tafi wannan Wadda ya Gina a cikin mazabunsa.

 

Alh. Darma ya Kara da Cewa Akwai fitilu da ya Samar Kuma ya Samar da Makarantu. Alh. Darma Ya jaddada cewa Wannan Asibitin Zata Koma tamkar Sabuwa inshallah yace Zasu Sanya gadaje da Duk Wasu kayan bukata insha Allah. Alh. Darma Yace Aiki Zai kammalu Nan da Mako Biyu Masu zuwa.

 

Dayake mika godiya Shugaban Asibitin Malam Usman yace “Suna samun kalubale dadama Sakamakon lalacewar Asibitin, Usman Yace Yasha ganin macizai a ciki Sakamakon lalacewar ta. Daga Bisani Yayi addu’a ga Hon. Salisu Iro isansi Allah ya Saka masa da Alkhairi.

 

Shima Kansila na Yankin Hon. Isiyaku Tasi’u ya tofa albarkacin Bakin yace “Duk Wata Matsala da take a word din to bayan wannan Asibitin take, amma Yanzu an share Masu kukansu. sana Yayi godiya ga Duk Wanda ya taimaka wannan aiki ya samu.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here