MATSALOLIN MAKARANTU DA YAJIN AIKIN MALAMAI A NAJERIYA: WASIKA ZUWA GA “YAN MAJALISUN DOKOKI

0

Bayan gaisuwa da fatan alheri a gare ku da yin godiya ga Allah, da kuma taya ku murna ta ganin wannan shekara, wadda ita ce ta Rarshe a wannan zango, na wa’adin wakilci da kuke mana.

 

Hakika kuna sane da irin mawuyacin halin da kasarmu ke ciki a yau, musamman Yajin Aikin malaman jami’oi da sauran manyan makarantu, wanda ya ki ci ya ki cinyewa.

 

Duk da yake mun sani kuna yin iyakar kokarinku game da shawo kan lamarin, sai dai zai yi wuya ku iya magance matsalar, saboda

kuwa ba ku san tushenta ba. Mun sani ko likita ba zai iya magance ciwo ba, muddin bai san tushensa ba. Dalilin haka ne muka rubuta

wannan littafi mai suna KWALLON MANGWARO, wanda zai haska muku, domin fahimtar tushen matsalar da kuma yadda za a magance ta. Dangane da sharrin matsalar kuwa, kamar yadda muka sani idan ta je ta dawo, duk abin a kan ‘ya’yan talakawa yake karewa, musamman yankinmu na Arewa wanda a halin yanzu karewa, muke a mawuyacin hali dangane da tattalin arziki da harkar tsaro, abu ne ba zai misaltu ba.

 

Hakika, dangane da wannan mummunan hali da jam’oinmu ke ciki a yau, ko kadan bai bambanta da irin yadda Hukumar NEPA, mai

samar wa kasa wutar lantarki ta shiga a shekarun baya ba, wanda daga karshe aka sayar da ita. Haka suma wadannan jami’oi namu na gwamnati, fargabarmu ita ce kar haka su ma ta kasance da su, a inda daga karshe za ta kai ga fagen an sayar da su.

 

Akwai bukatar masu girmaYan Majalisunmu su fahimci ce yawan yajin aiki, zai tilasta wadannan malamai na jamioi gwamnati su watsar da aikin jamia su samu wasu sana’o’, asu kuma su yi kaura zuwa kasashen waje ko su koma jami’oi Mas Zaman Kansu, wadanda a halin yanzu ake ta samarwa a wannan kasa, domin kuwa ko a jiha daya ta Arewa sai da muka kiyasta akwai sababbin jami’o’i Masu Zaman Kansu, a kalla har guda biyar, wadannan za su yi maraba da kwararrun malamai daga jami’ oin gwamnati.

 

Matsalar dai ita ce, jami’o’in gwamnati za su rasa kwararrun malamai. Mun kuwa sani da kudaden talakawa aka ilimantar da kuma horar da su wadannan malamai, wadanda rashinsu zai haifar da wagegen gibi a jami’o’in na gwamnati, wanda ba zai yiwu a iya cike shi cikin kankanen lokaci ba. Hasali ma dai hakan zai iya ida durkusar da jami’ oin, ta kai ga an rufe su ko sayar da su ga ‘yan kasuwa. Shin idan haka ta faru, ina makomar dubban dalibansu, da kuma miliyoyin yaranmu masu zuwa nan gaba? Me ke tasirin haka a harkokinmu na tattalin arziki da tsaro, wadanda a halin yanzu suke a mawuyacin hali. Wannan ita ce fargabar mu.

See also  AN KAI HARI CIKIN GARIN BATSARI TA JIHAR KATSINA

 

Daga karshe, ya ku wadannan Yan Majalisun dokoki namu masu girma, ku sani cewa matsalar da jami’ oinmu ke fama da ita da yajin aikin malamai, kasancewar haka ba laifin gwamnati ba ne ko na kungiyar malaman jami’ oi, a’a, laifin naku ne, saboda gazawar ku ta samar da sababbin dokoki, musaman wadanda suka danganci yadda gwamnati ke tafiyar da makarantun ta a wannan kasa. Watau dai, duk abin nan da ke faruwa game da durkushewar makarantu, da ku ya kamata mu yi kuka, ba da kungiyar malamai ta ASUU ko gwamnati ba.

 

Ya zama wajibi gare ku ku bar wa kan ku tarihi ta hanyar kasancewa ku ne kuka magance matsalar jami’oinmu da ma ta da sauran makarantun wannan kasa. Wannan kuwa abu ne mai saukin tabbatarwa ta hanyar yin dokoki game da tafiyar da makarantu kamar yadda muka bayar da shawara a cikin wannan littafi namu mai suna KWALLON MANGWARO. Akwai kuma bukata a gare ku ku jajirce wajen ganin gwamnati ta yi aiki da duk wasu tanade-

tanade da za ku yi game da tabbatar da abin. Hakika, duk tsawon shekarun nan da kuka yi a majalisa, a matsayin ku na wakilan mu, shin har akwai wani abu da kuka yi wa talaka, mai matukar alfanu da zai fi wannan. Ba mu da shakka cewa, saboda kishin kasar ku da

yankin ku, muna da kyakkyawan zato cewa, yin wadannan dokoki da tabbatar da an aiwatar da su, ba abu ne wanda zai kai mu ga

yin tsintsima a Eagle Square, ko yi maku ciri da cincirindo a mazabunku ba.

 

Wassalam

 

Aliyu M. Muri, PhD

GSM: 07083175058

 

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here