Suleman Umar
@ katsina city news
Dakta Muhammad Bara’u Tanimu dan takarar gwamna a jam iyyar Accord ya bayyana ma jaridun katsina city news cewa ya fito takara ne domin Al ummar katsina da tausayi da kuma kishin Halin da suke a ciki.
Tanimu Wanda yayi suna a katsina da wata Gidauniyar shi da yake taimakon al umma kyauta da ita mai suna island survive Foundation. Gidauniyar da ta dau shekaru tana aikin, baiwa matasa horon sana’ a da bada jari ga Mata masu kananan sana oi da kuma lokacin annobar korona suka bada kayan kariya.
Dakta Tanimu Wanda yake rike da sarautar walin kudun katsina,ya bayyana cewa.in ka dubi yadda jama’a suke a cikin hali.da kuma yadda mutane suka dawo daga rakiyar manyan jam iyyun da muke dasu guda biyu.
Jam’iyya irin ta a Accord itace mafita ga al umma.yace kuma a zaben 2023, za ayi zabe ne, bisa cancanta.ba dan takara ko jam iyya ba.
Walin kudun katsina,yace Ni haiffen unguwar tsohuwar kasuwa ce dake cikin birnin katsina.kuma ni kwararren masanin ilmin kidddigar gini ne.nayi aiki wurare kafin in koma gida don bayar da duk lokaci na ga Al ummar katsina.
Domin sauraren cikakkiyar hira jeka shafin Facebook na jaridun
Katsina city news da kuma jaridar taskar labarai ko you tube TV na wadannan shafukan.
Katsina city news
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
@ www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
@ www.thelinksnews.com
07043777779 08137777245