Sarkin Kano ya naɗa Sheikh Daurawa a matsayin limamin massllacin jami’ar Skyline

0

A safiyar jiya Alhamis ne, Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya naɗa babban malamin addinin Musuluncin nan, Sheikh Muhammad Aminu Ibrahim Daurawa, a matsayin babban limamin sabon masallacin jami’ar Skyline da ke tsohon ginin Bankin Arewa a Jihar Kano.

 

An yi bikin naɗin limancin ne a fadar Sarkin a Jihar Kano.

 

Daga isar shi fad’ar, Sheikh Malam Aminu Daurawa ya zarce ya gaida Sarki, sannan ya yi wa sarki addu’ar fatan alheri da fatan zaman lafiya ga al’ummar jihar Kano, da ma ƙasa bakiɗaya.

 

A wani abu da ba a saba gani ba a fada sosai, sarkin ya buƙaci su gaisa da malam Daurawa, inda kuma ya yi addu’a ta musamman tare da yaba wa Malamin game da ƙoƙarin wayar da kan mutane zuwa ga tafarkin Allah.

See also  SERAP Na Gargadin Shugaban Majalissar Dattawan Najeriya Kan Bukatar Gina Gidan Alfarma Ga Mataimakain Shugaban Kasar

 

“Mu na ganin irin abubuwan da mallam yake yi na wayar da kan al’umma da nusar wa. Mu na yi wa Malam godiya da addu’ar fatan alheri. Mu na ganin bidiyoyi na karatuttuka iri-iri, Allah Ya saka da alheri.” Inji Sarki.

 

Haka kuma bayan an naɗa Malam tare da na’ibansa guda uku, a masallacin fadar Sarkin Kano, tawagar Malam Aminu Daurawa ta dawo domin sake yi wa mai martaba Sarki godiya da addu’ar fatan alheri.

Majiya: daily Nigerian hausa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here