Ƴan Sanda Sun Fara Bincike Kan Wani Ɗan China Da Ake Zargi Ya Kashe Ummukulsum.

0

Rahotonni sunce Rundunar Ƴan Sanda Najeriya rashen jihar Kano ta ce ta kama wani ɗan asalin ƙasar China mai suna Geng Quanrong, mai kimanin shekaru 47 da ake zargi da kisan wata yar shekaru 22 mai suna Ummukulsum Sani wadda take zaune a unguwar Janbulo da ke jihar.

 

Kakakin rudunar yan sandan jihar Kano Sifiritandan yan sandan Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya tabbatar da kama wanda ake zargin a daren ranar Juma’ar data gabata.

 

Wanda ya ce yanzu haka kwamishinan jihar Kano ya bayar da umarnin a mayar da wanda ake zargin babban sashin binciken manyan laifuka domin a faɗaɗa bincike.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here