Muazu Hassan
@Katsina City News
Jaridun Katsina City News sun yi bincike da nufin gano ko akwai wata hujja ko doka da mazabar Kurfi ‘A’ ta bi wajen dakatar da mataimakin Shugaban Karamar Hukumar ta Kurfi Hon. Nazifi Rabe daga jam’iyyar APC, amma hakarmu ba ta cimma ruwa ba.
Bincikenmu ya gano tsohuwar gabar siyasa ce da ta dade tsakanin manyan ‘yan jam’iyyar APC a Kurfe ake son yi wa Hon. Nazifi Rabe bi-ta-da-kulli da ita.
Jaridunmu sun gano, tun bayan cin zaben fid da gwani na dan takarar shugabancin Karamar Hukumar, Nazifi ke fuskantar matsaloli, yayin da wanda jam’iyyar APC ta tsayar don takarar Shugaban Karamar Hukumar ya ki amincewa a Hukumar Zabe ta tantance shi da mataimakin nasa, inda mataimakin ya zo, amma Shugaban ya ki zuwa.
Bincikenmu ya gano, tun lokacin suka yi ta kokarin canza shi, amma aka ce doka ta hana. Shugaba da mataimakinsa igiya daya ce ta dauro su.
Bayan zaben na Kananan Hukumomi mai cike da takaddama, wanda yanzu haka maganar na kotu, sun duk hanyoyin da za su bi don dana wa Hon. Nazafi tarkon da za su kama shi, amma hakarsu ba ta cimma ruwa ba.
Majiyarmu ta gano tun da aka rantsar da su babu wani abin da ake da mataimakin, illa sanya masa ido da bugun cikinsa ana neman wata hujja ta murya da za a yi amfani da ita wajen tsige shi.
“Kasa samun wannan damar ta sa aka fara yi masa yarfen ba ya tare da jam’iyyar APC,” in ji majiyar tamu.
Hon. Nazifi ya rika shelantawa a kawo hujja ko ma wacce iri ce, ko da kuwa ta taimakon wani almajirin wata jam’iyya ce.
Binciken namu ya gano cewa zuwan dan takarar Gwamna a jam’iyyar APC, Dikko Umar Radda Kurfi ya kara rura wutar takaddamar.
A ziyarar, Hon. Nazifi ya taka rawa mai kyau wajen tayar sa da kyautata masa.
“Daga nan sai aka kafa masa wani kwamitin bincike a kan zargi ko tuhumar ba ya tare da jam’iyyar APC. Shi ma aka bincika babu hujja.
“A farkon makon nan aka aika masa takardar gayyatar ya bayyana gaban kwamitin bincike na zargin ba ya tare da jam’iyyar APC.
“Hon. Nazifi Rabe, ya halarci zaman kwamitin, ya kuma kalubalanci a kawo hujja ta murya, hoto, ko ma wacce irin hujja ce,” kamar yadda majiyar tamu da ta nemi a sakaya sunanta ta labarta mana.
Mun samu rahoton cewa a zaman kwamitin an bai wa Hon. Nazifi hakuri, tare da neman yafiyarsa.
Sai dai kuma jiya Juma’a sai aka saki takardar dakatar da shi daga jam’iyyarsa ta APC daga mazabarsa a bisa yanar gizo ba tare da an ba shi kwafi ba.
Ana zargin Shugaban Karamar Hukumar ne ya kitsa, tare da tabbatar duk wannan rashin bin ka’ida da rashin adalcin ya faru.
Mun kira wayar Shugaban don jin ta bakinsa, amma bai dauki wayar ba. Daga baya ma ya kashe ta.
Ana zargin an yaudari wadanda suka sa hannu ga wata takardar halartar mitin. Dayansu ya shaida mana cewa, an gayyace su ne kan wata magana suka sa hannu, sai aka yi amfani da takardar wajen dakatar da Hon. Nazafi.
Ra’ayoyin jama’a da muka samu a cikin Kurfi sun ce Nazifi dan APC ne na halas, wanda ya fi duk ‘yan APC mazauna Kurfi amfani ga taimakon asibiti ga tallafin karatu ga kuma sauraron matsalarka.
Suka ce suna gani zagon kasa ne ake wa APC a Kurfi domin wasu jam’iyyun su samu rabonsu.
A mazabar Kurfi A suna alfahari da dansu Hon. Nazifi Rabe, kamar yadda suka shaida mana.
Katsina City News
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar Taskar Labarai
@ www.jaridartaskarlabarai.com
The Link News
Www.thelinksnews.com
07043777779 08137777245