Gwamnan Borno, Farfesa Umara Zulum ya ce gwamnonin yankin Arewa-maso-Gabas na shirin kafa kamfanin sufurin jiragen sama na kasuwanci a yankin.
Farfesa Zulu, wanda ya zama Shugaban kungiyar Gwamnonin Arewa-maso-Gabas ya bayyana hakan a lokacin buɗe taronsu karo na bakwai a jiya Juma’a.
Zulum ya ce kamfanin sifirin jiragen na yankin zai taimaka wajen fadada iyakokin kasuwanci a yankin Arewa maso Gabas bayan shafe shekaru ana fama da matsalar rashin tsaro da ya hana yankin cigaba.
Gwamnan ya kuma yi tir da halin ko inkula da halin rashin gyara hanyoyin Gwamnatin Tarayya a yankin Arewa maso Gabas.
Zulum ya koka da yadda tashe-tashen hankula suka haifar da barna a yankin inda ya bukaci majalisar dokokin kasar da ta inganta kasafin kudin yankin domin taimakawa wajen sake gina yankin.
Da yake jawabi tun da farko Gwamnan Gombe Muhammad Inuwa Yahaya yace makasudin kafa kamfanin da ya shafe kimanin shekaru biyu ana tsarawa la’akari da nasarorin da aka samu tun da aka kirkiro.
Yahaya ya bayyana cewa har yanzu ana cigaba da samun kalubalen da suka kai ga kafa wani dandali dan magance abinda ke addabar yankin.
Ya kuma yabawa shugaban kasa Muhammadu Buhari kan kokarin da yake na dakile kalubalen tsaro dakuma kokarin da hukumomin tsaro keyi magance barazanar tsaro.
Majiya: daily Nigerian hausa