Jam’iyyar ADC ta kori ɗan takararta na shugaban ƙasa.

0

Gabanin zaben 2023, jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta kori dan takararta na shugaban kasa, Mista Dumebi Kachikwu daga jam’iyyar.

A makon da ya gabata ne dai jam’iyar ta dakatar da Kachikwu bisa wasu zarge-zarge.

Shugaban jam’iyyar na kasa, Ralphs Nwosu a wata sanarwa da ya fitar ya ce an kori Kachikwu ne saboda wasu abubuwa na zagon-ƙasa ga kundin tsarin jam’iyyar.

Ya ce kwamitin mutum bakwai da jam’iyyar ta kafa wanda ya shafe kwanaki shida yana aiki, ya mika rahotonsa a ranar Alhamis.

Nwosu ya ce a ranar Juma’a ne kwamitin ayyuka na jam’iyyar (NWC) ya tattauna kan rahoton tare da karɓar rahoton kwamitin tare da gyara a kai.

See also  Asiwaju Bola Ahmed Tinubu Ya Lashe Zaben Fitarda Gwani APC

Sauran mutanen da aka kora daga jam’iyyar sun haɗa da Kennedy Odion, Kingsley Oggah, Musa Hassan, Bello Isiyaka, Clement Ehiator, Kabiru Hussaini da Alaka Godwin

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here