Osinbajo ya tafi Ingila don halartar taron binne Sarauniya Elizabeth

0

Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya tashi zuwa kasar Ingila domin halartar taron binne gawar marigayiya sarauniyar Ingila Elizabeth ta ll.

 

A takardar da mai baiwa Osonbajo shawara kan yaɗa labarai, Laolu Akande ya fitar a yau Asabar, ya ce Osinbajo a taron na ranar litinin, zai haɗu da sauran iyalan masarautar Buckingham da Shugabanin duniya da ma sauran manyan baki dan shaida yadda za binne Sarauniyar.

 

Sanarwar tace Osinbajo Yana daga cikin manyan baki da Sarkin Ingila Charles na III da matarsa Camilla za su tarba a fadarsu ta Buckingham.

 

Akande ya ce Osinbajo zai dawo Nijeriya ranar litinin bayan kammala janaizar Sarauniyar.

See also  Bello Matawalle ya yabawa Gwamna David Umahi da ya fice daga jam’iyyar PDP

 

A ranar 8 ga watan Satimbar Elizabeth ta ll ta mutu a Balmoral Castle dake Scotland a Burtamiya tana da shekara 96 a duniya

 

Kafin mutuwarta, ita ce shugabar ƙungiyar ƙasashe rainon Ingila ,Kuma wacce tafi kowa jimawa a kan Gadon mulkin sarautar Ingila da shekara 70.

Majiya: daily Nigerian hausa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here