Muazu hassan
@ katsina city news
Shugabannin mazabar kurfi A dake karamar hukumar kurfi sun tsige shugaban mazabarsu Alhaji Aliyu Muhammad bisa zargin ya dauki wani mataki na dakatar da Hon Nazifi Rabe, ba tare da bin kaida ko tuntubarsu ba.
Takardar wadda shugabannin su Goma sha hudu suka Sanya ma hannu.sun Nada sakataren mazabar Dahiru Rabe a matsayin sabon shugaba.
Jaridun katsina city news sun samu tabbacin, sabon shugaban har ya fara aikin shi.har ya rubuta takarda wadda ya Sanya ma hannu na sanar da duk Wanda ya cancanta cewa an samu chanji.
Sabin shugabannin sun dage dakatar da tsohon ciyaman yayi wadda aka yi ta ba bisa kaida ba.
Katsina city news
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
@ www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
@ www.thelinksnews.com