Yadda dan China ya hallaka Ummita a Kano

0

Freedom Radio ya Ruwaito Cewa Hukumomi a Kano sun cafke wani dan kasar China mai suna Mr Geng bisa zargin hallata wata mata Ummukulsum Buhari da aka fi sani da Ummita a unguwar Janbulo Dake Cikin Garin kano

 

Rahotonni sun ce, Mr. Geng wanda tsohons Ummulkhairi ne ya kutsa kai cikin gidansu a daren Jumu’a, inda ya caka mata wuka.

 

An garzaya da ita asibitin UMC da ke Janbulo, a nan ne kuma rai yayi halinsa.

Wani makusancin marigayiyar ya ce, sun shafe shekaru biyu suna soyayya da Mr Geng kafin ta yi aure da wani.

 

Sai dai daga bisani auren nata ya mutu, amma shi Mr Geng bai daina bibiyarta ba.

 

Tuni dai jami’an hukumar shige da fice ta kasa suka cafke Mr Geng tare da mika shi ga yan

sandan kano domin ci gaba da bincike.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here