An naɗa gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, a matsayin shugaban matasan tawagar yakin neman zaɓen Tinubu-Shettima a jam’iyyar APC.
Vanguard ta ruwaito cewa wannan naɗin na cikin wata takarda mai adireshin Yahaya Bello ɗauke da sa hannun ɗan takarar shugaban ƙasa na APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
A takardar Tinubu ya jaddada cewa gwamna Bello na ɗaya daga cikin manema tikitin takara a zaɓen fidda gwanin APC ta suka cancanci wannan babban matsayi duba da nasarorinsa a matsayin gwamna da mamban jam’iyya.
Tsohon gwamnan Legas ya ƙara da cewa gwamnan na Kogi zai yi duk me yuwuwa wajen sauke nauyin da aka dora masa da isar da sakon Kamfe, wanda zai zama fitila ga nasara a 2023.
Idan baku manta ba gabanin zaɓen fidda gwanin APC, mata da matasa daga dukkan shiyyoyi shida na Najeriya sun ayyana goyon bayansu ga Yahaya Bello.
Majiya: Hausa Legit