Kotu Ta Tasa Keyar Wani Mutum A Benume Zuwa Gidan Gyaran Hali Saboda Zambar N7m

0

Kotu Ta Tasa Keyar Wani Mutum A Benume Zuwa Gidan Gyaran Hali Saboda Zamba N7m

 

Mai shari’a A.R Mohammed na babbar kotun tarayya a Makurdi, jihar Benue ya yanke wa James Ebute Adejoh hukuncin zaman gidan gyaran hali bayan ya kama shi da laifin zambar kudi ta POS kimanin Naira miliyan bakwai da dubu dari da goma sha takwas.

 

Mai shari’ar ya yanke masa hukuncin ne bayan Wanda ake zargin ya amsa laifin nashi akan tuhuma daya da hukumar EFCC shiyyar Benue ta gabatar akan shi.

 

Mai shari’ar ya yanke masa hukuncin shekara daya a gidan gyaran hali ko yabiya tarar Naira dubu dari biyar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here