Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 1, Sun Yi garkuwa da Manoma 3 A Kaduna

0

Wasu ‘yan bindiga sun kashe mutum daya tare da yin garkuwa da wasu manoma uku a kauyen Kurgin Gabas da ke karamar hukumar Birnin Gwari a jihar Kaduna.

 

Shugaban kungiyar cigaban masarautar Birnin Gwari (BEPU), Ishaq Usman Kasai ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Kaduna.

 

“A ranar Alhamis 15 ga Satumba, 2022 ‘yan bindiga dauke da makamai sun yi garkuwa da wasu mutane uku a gonaki a yankin Kurgin Gabas da ke yammacin karamar hukumar Birnin-Gwari ta jihar Kaduna.

 

“’Yan bindigan sun kuma kai farmaki a unguwar a ranar Juma’a 16 ga wata, sun sace babur (Bajaj Model) tare da kashe mai shi (Bala Balansi) nan take kafin su koma dajin.

See also  Maikudi Decries Marginalisation Of Women In Politics, Economy

 

“Kurgin Gabas na kan iyaka da dajin Kamuku wanda ya zama maboyar ‘yan fashi da makami kuma hanya ce ta gama gari da ‘yan fashin ke fitowa daga maboyarsu domin kai hare-hare a yankunan yammacin Birnin-Gwari da kuma makwabtan Rafi. Karamar Hukumar Neja.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here