CIBIYAR YUSUFU BALA USMAN ZA TA KADDAMAR DA LITTAFI MAI SUNA “FUSKAR KUNCI DA TALAUCI A NIJERIYA” 

0

Daga Danjuma Katsina

 

Cibiyar Yusufu Bala Usman mai hedikwatar ta Zariya a jihar Kaduna, za ta kaddamar da wani littafi na kundin binciken irin yadda talauci da kuncin rayuwa ya yi katutu a Nijeriya.

Binciken, wanda Cibiyar ta yi da tallafin Gidauniyar Rosa Luxembourg da ke kasar Jamus, an gudanar da zuzzurfan bincike a jihohin kasar nan, wanda aka tattauna kai tsaye da mutane a kan halin da talauci da kuncin rayuwa da suka yi katutu a Nijeriya.

 

Cibiyar ta dauki mutane daban-daban a jihohi, wadanda suka tattara mata bayanai kai tsaye a murya, hoto da kuma bidiyo.

Sannan wadansu kwararru suka zauna tsawon lokaci suka bi duk bayanan suka fito da kundin littafin da za a gabatar.

See also  Malam Gambo Muhammed (RATIBI) ya zama sabon limamin babban masallacin juma'a

 

Za a yi taron ne a ranar 21 ga watan Satumba 2021, kuma mutane za su iya bin taron daga ko’ina suke a duniya.

 

Za a yi taron ne ta yanar gizo daga Nijeriya da duk inda kake a duniya.

 

Wadanda za su tattauna a kan littafin sune Farfesa Mike Kwanishie, Dakta Hauwa Mahdi, Dakta Hussaini Abdu, Mr. Owei Lakemfa, da Dakta Clause Dieter Konig.

 

Wannan aikin shi ne irin sa na farko da wata Cibiyar ilmi ta taba gabatarwa a Nijeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here