Gidan Wani Shugaban Kasa yanzu ya koma gidan beraye, jemagu da maciji

0

Wannan gidan da kuke gani gidan tsohon shugaban kasar Zaire ne Wanda yanzu ana kiran kasar da suna DRC, Ance Shugaban Yayi mulkin kama karya, sunan Shugaban Ƙasar Field Marshal Mobutu Sese Seko Kukungbendu Wazabanga.

 

Kyakkyawar tsarin da aka gina gidan sa akan wani babban fili (sai kace wurin shakatawa ne) an gina wannan waje ne a ƙauyen su, ana kiran gidan da suna Gbadolite, Gidan ya lakume Sama da £100m.

 

An ƙawata babban gidan da marmara, sana Yana da Tsarin sadarwar fasahar fasaha na Iseea da wurin shakatawa da filin jirgin sama, Kuma duka gilashin gidan baya jin Bindiga, da wurin shakatawa mai cike da kowane nau’in namun daji.

See also  FCTA ta kulle kasuwar Dutsen Alhaji har sai baba-ta-gani

 

Kafin Shugaba Mobutu ya Mutu Wajen ya kasance ɗaya daga cikin manyan gine-gine masu zaman kansu da wani shugaban ƙasa ya taɓa mallaka, yanzu gidan ya zama gidan beraye da macizai da sauran namun dajin.

 

mukasance a wani sabon shiri Daga naku Muhammad Kabir

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here