NDLEA Ta Bankado Babban Dakin Ajiye Hodar Iblis, Wacce Takai Darajar N193bn

0

Jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi, NDLEA, ta farmaki wani babban dakin ajiya a yankin Ikorodu da ke jihar Lagas inda aka kama hodar iblis da ya kai nauyin tan 1.8 (kilo 1,855).

Darajar wannan hodar iblis da aka kama a dakin ajiyar ya kai $278, 250,000 wanda yayi daidai da biliyan N194, 775,000,000, jaridar PM News ta rahoto.

Akalla masu fataucin miyagun kwayoyi hudu ciki harda dan kasar Jamaica da manajan dakin ajiyan aka kama a shiryeyen harin wanda ya shafe tsawon kwanaki biyu a wurare daban-daban a jihar Lagas.

Mutanen da aka kama sun hada Messrs Soji Jibril, mai shekaru 69 dan Ibadan jihar Oyo; Emmanuel Chukwu, mai shekaru 65 daga Ekwulobia, jihar Anambra; Wasiu Akinade, mai shekaru 53 daga Ibadan, jihar Oyo.

Sauran sune Sunday Oguntelure, mai shekaru 53, daga Okitipupa, jihar Ondo da kuma Kelvin Smith, mai shekaru 42, dan asalin Kingston, Jamaica. Dukkaninsu mambobin kungiyar hada-hadar miyagun kwayoyi da hukumar ke bibiya tun a shekarar 2018.

An farmaki rumbun wanda ke a gida mai lamba 6 Olukuola crescent, Solebo estate, Ikorodu, a ranar Lahadi, 18 ga watan Satumba. An kuma kama masu harkar a masauki da mabuyarsu da ke wurare daban-daban na Lagas tsakanin daren Lahadi da safiyar Litinin, 19 ga watan Satumba.

Majiya: hausa legit

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here