Jaridar daily Nigerian hausa ta Ruwaito Shugaban Ƙaramar Hukumar Okene na jihar Kogi, Injiniya Abdulrazaq Muhammad, na kira ga jami’an tsaro da su kama tare da bincikar wanda ya kafa wata majami’a mai suna ‘New Jerusalem Deliverance Ministry’, Fasto Peter Michonza.
Hakan ya zo ne biyo bayan kiraye-kirayen da a ke yi ga gwamnatin jihar, kungiyar kiristoci ta Najeriya, da kungiyar likitocin Najeriya da su duba ayyukan faston bayan faifan bidiyonsa ya na sayar da “ruwa mai hana shigar harsashi” ya yadu.
Shugaban, a cikin wata sanarwa, ya lura cewa umarnin na gudanar da bincike ya zama dole “bayan wasu jama’a da abin ya shafa sun wallafa wasu ayyukansa na rashin tsoron Allah a shafukan sada zumunta.”
Yayin da ya ke yaba wa jama’a da suka yi ta fallasa irin ta’asar da ake zargin Mista Peter da aikatawa da sunan ayyukan coci, Muhammad ya yi alkawarin cewa za a bayyana cikakken bayanan binciken nan gaba kaɗan.
Faifan bidiyon fasto Peter Michonza ya yi ta yawo a kafafen sada zumunta da ake zargin ya na gudanar da aiyuka ga mata masu juna biyu a Cocinsa da kuma sayar wa jama’a ‘ruwan maganin harsashi’, da sauran ayyukan da ba su amince da magani ba wadanda suka yi sanadin mutuwar mutane da dama.
A baya dai Michonza a wata zanga-zangar da ‘yan kungiyarsa suka gudanar a Okene, ya yi kira da a saki mawakin kasar Amurka, R.Kelly wanda aka daure a kwanan baya bisa laifin lalata da yara da kuma zargin fyade.
Majiya: daily Nigerian hausa