Rundunar Ƴan Sanda a jahar katsina Sunyi Nasarar kama Wasu Barayi, Kamar yadda Mai Magana Da Yawun Rundunar SP Gambo Isah ya Shaida Ma Jaridar Taskar Labarai.
Yace “A ranar 12 ga watan satumba 2022 Barayin sunje Garin Daura Domin suyi halin Nasu sai dubun su ta cika Sukayi Karon Batta da jami’an Ƴan Sanda.
Gambo Ya Kara Da cewa “Barayin Baki ne ba Yan asalin karamar hukumar Daura bane, Biyu Daga cikin su sun fitone Daga Hadeja ta Jigawa Sai Dayan ya fito Daga Badawa a jahar Kano.
An Biyo Barayin ne Sai Suka Haura Katanga Ashe Basu Saniba wannan Katangar ta Ƴan Sanda ce Wacce take A Sabon Gari a cikin karamar hukumar Daura.
Daga cikin wadan da Ake zargi Akwai Abdullahi Sa’idu Dan shekara Hamsin (50) sai Umar abubakar Faruk Da Husain yan shekara 25