Ambaliyar ruwa na barazanar ɗaiɗaita al’ummar Hadejia

0

A cikin daren jiya Talata ne dai hankali ya tashi a garin Hadejia inda ruwa yai barazanar yin ambaliya a garin.

 

Daily Nigerian Hausa ta jiyo cewa cikin daren ne dai, da misalin karfe 12, al’umma dake cikin Garin Hadejia suka fita suke aikin jinga (buhunan ƙasa da a ke tare ruwa da su) har zuwa asuba.

 

Abin da ya haifar da matsalar shi ne karyewar da jingar ruwa ta yi, wanda ta ke tunkarowa maƙabartar makarantar bayan gari, da kuma cikin garin na Hadejia.

 

Sama da mutane 5,000 ne su ka halasci wajen gyaran jingar a cikin wannan dare, in ji mazauna garin.

See also  FG to build 500 homes in Bauchi

 

Sun ce fitowar mutanen na da nasaba da kiran sallah da aka riƙa yi a masallatai da ke cikin garin Hadejia, da kuma gudunmawar da tashar Sawaba Radio ta bayar, inda ta kwana ta na magana kan batun Jingar ruwan da ya ke mamaye al’ummar Jigawa.

 

“Muna bukatar addu’a daga bakunan y’an uwa musulmi domin muna cikin masifa, damu da makwabtan k’auyuka da garurukan da ke kusa damu, wanda ruwan sama ya yi gaba da gidaje, gonaki, dukiya, dakuma rayukan Al’umma,” in ji wani mazaunin garin, Saleh Shehu Hadejia.

Majiya: daily Nigerian hausa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here