Babu Tabbacin Ahmad Lawan Zai Dawo Majalisa, ya fara Takara Tun 1999

0

Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Ahmad Ibrahim Lawan bai cikin sunayen ‘Yan takaran da hukumar zabe na INEC ta fitar a makon nan.

 

A ranar Talatar nan Hukumar zabe ta wallafa sunayen wadanda za su shiga takarar shugaban kasa, majalisar dattawa da majalisar wakilai a zabe mai zuwa.

 

A Cewar Jaridar Legit.ng Hausa ta bi sunayen ‘yan takaran da za a gwabza da su, ta fahimci idan aka tafi a haka, Ahmad Ibrahim Lawan ba zai yi takarar komawa majalisa ba.

 

Rikicin shugaban majalisar da Hon. Bashir Machina ya yi sanadiyyar da jam’iyyar APC ta rasa ‘dan takarar kujerar majalisar dattawa a yankin Yobe ta Arewa.

See also  Ambaliyar ruwa: Sarkin Musulmi ya nemi 'yan Najeriya su cigaba da addu’a don gujewa sake faruwar ambaliyar ruwa

 

A gefe guda kuma, mun ga cewa Sanata Ibrahim Gaidam da Bomai Ibrahim Mohammed za suyi wa APC takarar Sanatoci a Gabas da Kudancin Yobe.

 

Tun 1999, Ahmad Lawan ya zama ‘dan majalisar wakilai na shiyyar Bade da Jakusko. A 2003 ya zama Sanata da Usman Albashir ya nemi takara Gwamna.

 

Idan har Lawan bai samu tikitin majalisar dattawa a zabe mai zuwa ba, wannan zai zama karon farko tun shekarar 1999 da bai tsaya takara a jihar Yobe ba. Kamar Yadda legit hausa ta Ruwaito.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here